Rikicin Doguwa/Garo: Jiga-jigan APC na Doguwa sun ziyarci Murtala Sule Garo

0
68

Hotunan ziyarar ban hakuri da shugabannin masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC na karamar hukumar Doguwa suka zo domin bada hakuri ga dan takarar mataimakin gwamnan Jihar Kano Alhaji Murtala Sule Garo bisa rashin albarkar da Alasan Doguwa yayi masa.

Sanata mas’ud El-Jibril Doguwa shine ya jagoranci tawagar tare da Dan majalisar jiha mai wakiltar Doguwa, Hon. Salisu Mohammed da tsohon kwamnina Hon. Usman Sule Riruwai da mataimakin shugaban Jam’iyya Alh. Shehu Maigari, da shugaban karamar hukumar Doguwa, Alh. Mahmuda Hudu da Shugaban Jam’iyyar Apc na Doguwa sauran Jagororin Jam’iyya.

Shugabbannin sunyi bayani na nuna rashin jin dadin su da kuma rokon Alhaji Murtala Sule yayi hakuri sannan suka tabbatar da zasu dauki matakin daya dace tun daga tushe.