Ministar kudi na yiwa yaki da Rashawa zagon kasa a Najeriya – Majalisar wakilai

0
59

Majalisar Wakilai ta zargi Ministar Kudi, Zainab Ahmed da Akanta-Janar na Kasa, Sylva Okolieaboh da Kuma Darakta-Janar na Ofishin Kasafin kudade, Ben Akabueze da yin kafar ungulu ga yaki da rashawa a Najeriya.

Majalisar ta yi zargin ne tare da sanya kalubalantar dalilin ware wa hukumomi masu ‘dumama kujera’ makuden kudade’ a kasafin 2023, amma suka zaftare fiye da rabin kasafin Ofishin Mai Binciken Kudi na Kasa.

Hakan ta taso ne bayan mukaddashin Mai Binciken Kudi na Kasa, Andrew Okwudili, ya yi mata korafi cewa Ofishin Darakta-Janar kan Kasafi ya yi wa Ofishinsa kwauron kudi, duk kuwa da “matsayinsa na babbar hukumar bibiyar hukumomin tara kudaden shigar Gwamnatin Tarayya.

“Babbar Hukuma irin wannan tana bukatar isassun kudaden da kayan aiki da duk abubuwan da suka dace domin gudanar da ayyukanta yadda ya kamata,” in ji shi.

Ya bayyana haka ne a lokacin da yake kare kasafin kudin ofishin na 2023 a gaban Kwamitin Kudade na Majalisar Wakilai a ranar Laraba.