Kwastam ta kama kayan fasa kauri da kudinsu ya kai miliyan 78.6 a Kebbi

0
60

Hukumar Hana Fasa Kwauri ta Kasa (NCS) a Jihar Kebbi, ta kama wasu kayayyakin fasa kwauri da kudinsu ya kai Naira miliyan 78.6 a watan Oktoban 2022 a jihar.

Shugaban hukumar Kwastam, Mista Joseph Attah ne ya bayyana haka a lokacin da ya ke zantawa da manema labarai a kan ayyukan hukumar na watan Oktoba a Birnin Kebbi.

Ya ce rundunar ta samu nasarori a cikin muhimman ayyukan da suka shafi aikin dakile fasa kwauri, ta samar da kudaden shiga da kuma saukaka kasuwanci.

A cewarsa: “An ci gaba da samun karuwar kudaden shiga na hukumar. A tsawon lokacin da ake bitar, mun samar da zunzurutun kudi har Naira miliyan 162.2 a matsayin kudaden shiga daga harajin shigo da kayayyaki. Wannan shi ne mafi girma tun bayan bude iyakar ta Kamba da ke a Jihar ta Kebbi.

“Rundunar ta kuma taimaka wajen fitar da kayayyakin da ake sarrafa su a cikin gida na sama da Naira biliyan 2 a daidai lokacin da ake gudanar da bincike,” in ji Attah.