HomeLabaraiAn cire kwamishinan ’yan sandan Kano kan zargin rashawa

An cire kwamishinan ’yan sandan Kano kan zargin rashawa

Date:

Related stories

INEC ta ayyana 29 ga Maris a matsayin ranar zaben cike gurbi a Adamawa

Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC), ta...

IPOB ta umarci ‘yan kabilar Igbo da ke Legas su koma gida

Kungiyar masu rajin kafa ‘yantacciyar kasar Biafara ta IPOB,...

Sarkin Kano ya taya Abba Kabir murnar lashe zaben gwamnan Kano

Sarkin Kano Aminu Ado Bayero ya taya Abba Kabir...

Mata magoya bayan PDP na zanga-zangar kin amincewa da zabe a Kaduna

Wata tawagar mata sanye da bakaken kaya na jam’iyyar...
Wata biyu kacal da nada Abubakar Lawal a matsayin Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Kano, an cire shi kan zargin rashawa.
Shugaban ’Yan Sandan Najeriya Usman Baba, ya mayar da Abubakar Lawal Jihar Ebonyi, bayan samun sa da laifin; nan take aka maye gurbinsa da takwaransa na Ebonyi, Aliyu Garba.

Wata majiya mai tushe ta shaida wa Aminiya cewa akwai zargi kan CP Lawal cewa tura shi Kano a watan Agusta ke da wuya, “Sai ya dauke duk wasu bincike da ke alamar tsoka zuwa ofishinsa.

“Sannan ya sanya harajin mako-mako ga duk muhimman sassan da manyan ofisoshin ’yan sanda ke karkashin rundunar — abin da ya fusta shugaban ’Yan Sandan Najeriya.”

Aminiya ta samu rahoto cewa mataimakan Kwamishinan ’Yan Sanda da aka sauya wa wurin aiki ne suka aike wa shugaban ’yan sanda rahoton rashawar da ke gudana a karkashin sabon kwamishinan.

Bayan nan ne Hedikwatar ’Yan Sanda ta Najeriya ta sa a yo binciken kwakwaf a sirrance, wanda a karshe ya tabbatar da zargin da ake wa sabon kwamishinan.

Wata majiya mai tushe ta ce Shugaban ’Yan Sandan da kansa ya zauna da wasu daga cikin masu zargin, a lokacin binciken, da nufin gano gaskiya.

A watan Agusta ne dai aka tura CP Abubakar Lawal zuwa Jihar Kano, bayan magabacinsa, ya yi ritaya daga aiki.

Wakilinmu ya nemi karin bayani kan lamarin daga kakakin ’yan sandan Najeriya, Muyiwa Adejobi, amma ya ce ba shi da masaniya.

Amma mun samu gabin wani sako da Hedikwatar ’Yan Sanda ta aike a ranar Juma’a mai lamba, TH.5361/FS/FHQ/ABJ/V.T3/87, cewa sauyin wurin aikin ya fara aiki ne nan take.

A halin da ake ciki ranar Litinin sabon kwamishin da aka tura Kano, Aliyu Garba, zai fara shiga ofis.

Sabon Kwamishinan ’yan sandan Kano, a baya ya kasance Mataimakin Kwamishina mai kula da Walwala, Kudade da Gudanarwa a Hedikwatar Rundunar da ke Abuja.
AMINIYA

Subscribe

- Never miss a story with notifications

- Gain full access to our premium content

- Browse free from up to 5 devices at once

Latest stories