Karin yara miliyan 15 na cikin hadarin kamuwa da cutar Tamowa a Najeriya – UNICEF

0
68

Asusun tallafawa kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF ya yi gargadin cewa kananan yara miliyan 14 da dubu 700 a Najeriya galibinsu ‘yan kasa da shekaru 5 da haihuwa na cikin hadarin kamuwa da cutar Tamowa wadda karancin abinci me gina jiki ke haddasawa.

UNICEF ta bayyana cewa idan har ba a dauki matakan da suka kamata ba, a shekarar da muke shirin ban kwana da ita, yara miliyan 13 za su fuskanci cutar tamowa yayinda wasu miliyan 1 da dubu 700 kuma za su fuskanci matsananciyar cutar ta Tamowa galibi a yankin arewacin Najeriyar

Asusun na UNICEF ya ce abin takaici ne yadda alkaluma ke nuna mutuwar kananan yara 100 ‘yan kasa da shekaru 5 da haihuwa duk bayan sa’a daya a Najeriya, yayin da wasu yaran na daban miliyan 12 ke cikin halin matsanancin rashin abinci.

Shugabar sashen abinci mai gina jiki ta UNICEF a Najeriya Nemat Hajeebhoy, ta ce yara a Najeriya na halin tsananin bukatar abinci mai gina jiki lura da yanayin da kasar ke ciki na tabarbarewar tattalin arzki da ya sanya iyalai gaza sabun isasshen abinci.

A cewar jami’ar matsaloli masu alaka da ambaliyar ruwa da ta lallata tarin amfanin gona a sassan Najeriya na shirin sake tsananta karuwar yaran da ke fama da wannan cuta ta rashin isasshen abinci mai jiki wato cutar yunwa ko kuma Tamowa.