Dala na gab da zarta Naira dubu – Najeriya

0
57

Darajar Naira ta ci gaba da faduwa a karshen wannan makon, inda a yanzu farashin Pam daya na Ingila ya zarta Naira dubu daya a kasuwannin bayan fage.

Ana fargabaar cewa, ita ma  Dalar Amurka za ta zarta Naira dubu 1 kowanni lokaci daga yanzu.

A makon jiya ne Hukumar da ke Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta kasarnan ta kai samame a kasuwannin ‘yan canji a Lagas da Abuja da Kano bisa zargin su da haddasa tsadar farashin kudaden ketare a kasar.

Sai dai ‘yan canjin sun mayar da martini, inda suka ce tsare-tsaren gwammati ne ya jefa kasar cikin halin da take ciki.