NDLEA ta kama makaho dan Nijar da safarar miyagun kwayoyi

0
61

Jamiā€™an Hukumar NDLEA mai yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi a Najeriya ta sanar da kama wani mutum makaho da dansa yayin da suke kokarin safarar tabar wiwi da miyagun kwayoyi.

Cikin wani sako da NDLEA ta wallafa a shafinta na Facebook dauke da sa hannun Darektan yada labaranta, Femi Babafemi ta ce an kama mutanen biyu ne a hanyar Malumfashi Zaria a Jihar Katsina.

NDLEA ta ce mahaifin wanda shi ne makahon mai shekaru 52 da dansa mai shekaru 30, dauke da kilo 20.5 na tabar wiwi da kuma gram 10 na exol-5.

NDLEA ta bayyana cewa asalin mutanen sun fito ne daga Jihar Damagaram da ke Jamhuriyar Nijar.

Kazalika, NDLEA ta ce jamiā€™anta na sintiri ne suka cafke mutanen a hanyarsu ta komawa Nijar.