Ya kamata a shigo da Hisbah don magance daba a harkar kamfe

0
61

Duba da yadda al’amuran daba da shaye-shaye a tsakanin al’umma ke kara ta’azzara musamman gabannin zabukan shekarar 2023, wani dan gwagwarmaya kuma mai bincike, Ibrahim Garba Maryam, ya bukaci a shigar da ’yan Hisbah harkokin kamfe din ’yan takara.

Maryam, ya yi wannan tsokaci ne a yayin da Hukumar Gidan Rediyon Arewa da ke Kano ta shirya wani taro domin nemo masalaha ga matsalolin ka iya kawo tasgaro ga zaben shuganni a shekarar 2023 da aka yi wa taken “2023: Makomar Najeriya.”

Ya bayyana cewa, ’yan siyasa da gwamnati na daga cikin wadanda suke saka al’amuran daba da shaye-shaye ke samun muhalli a cikin al’umma, saboda haka akwai bukatar jami’an Hisbah su shiga harkokin kamfe.

“Batun shaye-shaye da dabanci a Jahar Kano ya kamata mu fada wa kanmu gaskiya.

“’Yan siyasa su suke haddasa mana wannan shaye-shaye saboda duk dan siyasa daga kan gwamna zuwa sanata da shugaban kasa, duk mai neman takara sai ka gan shi da mota guda ta ’yan daba.

“Yanzu idan gwamna zai fita, za ka gan shi da motar KAROTA, Road safety da ’yan sanda, amma ba za ka gan shi da motar Hisbah ba, saboda an san Hisbah suna kama ’yan maye, kar su je a kama musu yara.

“In dai za a tsaftace harkan nan, a daina yawo da yara ’yan daba da masu shaye-shaye da sauransu.

“Wannan kalubale ne ga Gwamnatin Jihar Kano, da saninta ake wannan shaye-shayen?

“Mafita ita ce a yi doka, duk dan siyasan da zai wuce, a bar ’yan sanda da ’yan Hisbah su kama ’yan shaye-shaye; Idan mutum ya ga yana fita ana kama shi, za a samu canji.

“A karawa Hisbah kudi da ma’aikata domin a yaki wannan mummunar dabi’a.