Wani mahaifi ya banka wa ‘ya’yan matarsa 5 wuta kan sabani da mahaifiyarsu a Ondo

0
110

Wani mahaifi dan shekara 54 a duniya, Mista Ojo Joseph ya fada komar ‘yansanda bisa zarginsa da banka wuta kan ‘ya’yan matarsa su biyar a yankin Fagun Crescent da ke cikin birnin jihar Ondo.

Mutumin an yi zargin cewa sun samu sabani da matar tasa wacce kuma ita ce mahaifiyar yaran biyar da har ya ke ganin ta masa laifi, lamarin da ya kaisa ga daukan wannan mummunar matakin.

An kuma gano cewa Joseph ya shiga da man fetur cikin dakin yaran a lokacin da suke barci inda ya banka musu wutar kuma daya daga cikin yaran ya kone kurmus har lahira.

Sauran hudu daga cikin yaran suna kan amsar kulawar Likitoci a asibitin Gwamnatin tarayya da ke Owo yayin da mahaifiyar tasu da ‘yan tagwayen ‘yan watanni 18 suka tsallake rijiya da baya daga wutar tare da samun kananan raunuka.

Da take tabbatar da faruwar lamarin, jami’ar watsa labarai ta rundunar ‘yansandan jihar, Mrs Funmi Odunlami, ta ce mutumin ya shiga hannun hukumarsu bisa zargin kisan kai.