Zaben 2023: Za a raba wa ’yan sanda sabbin kayan aiki

0
118

Babban Sufeton ’Yan Sandan Najeriya, Usman Baba ya ba da umarnin da a soma rarraba wa ’yan sanda kayan aiki ba tare da bata lokaci ba, domin tunkarar babban zaben mai zuwa.

Kayan kwantar da tarzomar da za a raba sun hada da riguna da hular kwano masu sulke da hayaki mai sa hawaye da bindigar harba ta da kuma bindiga mai kashe lakka.

Sanarwar da kakakin rundunar, Muyiwa Adejobi, ya fitar ranar Litnin ta ce shugaban ’yan sandan ya kuma bayar da umarnin a raba musu sabbin kaki da sauran kayan aikin da suka kamata.

Sannan ya kuma yi kira ga jami’an rundnuar da su yi amfani da kayayyakin su yi shigar da ta kamata domin kare martaba da kimar aikinsu kafin, a lokacin da kuma bayan zaben na 2023.

Sannan ya yi kira a jami’an da su nuna halin da’a da kwarewa da kuma sanin ya kamata, kar su take hakkin jama’a a yayin gudanar da aikinsu.