Ambaliyar ruwa: Kasar Jordan ta bai wa Najeriya kayan tallafi

0
56

Biyo bayan bala’in ambaliya da ta addabi al’umomi da dama a kasar nan a cikin ‘yan kwanakin nan, Masarautar Jordan ta hannun wata kungiyar agaji ta Jordan Hashemite, ta bai wa Nijeriya tallafin kayayyakin agaji iri-iri.

Kayayyakin da aka bayar a karkashin umarnin Sarki Abdullah na II bin Al-Hussein Al Hashimi na Kasar Jordan da rundunar sojojin sama ta Royal Jordan ta kai wa gwamnatin tarayya kayan sun hada da kunshin kayan abinci da tufafi da barguna da kayan tsaftar jiki.

A wata sanarwa da shugaban sashen yada labarai na hukumar bayar da agajin gaggawa ta kasa (NEMA), Manzo Ezekiel, ya fitar, ya ce wani jirgin saman Hercules C130 na rundunar sojojin sama na Masarautar Jordan da ke jigilar kayayyakin agajin ya isa bangaren dakon kaya na filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe, Abuja da misalin karfe 7: 45pm na daren Laraba.

Da yake karbar kayayyakin, a madadin gwamnatin tarayya, babban daraktan hukumar NEMA, Mustapha Habib Ahmed, ya yaba da irin wannan karamcin da Sarkin Jordan, da gwamnati da al’ummar Masarautar suka yi wa Nijeriya, musamman a halin da ake ciki a halin yanzu da ake ciki, don tallafa wa mutanen da ambaliyar ta rutsa da su.

Ahmed ya kuma mika godiyar shugaban kasa Muhammadu Buhari da ministar harkokin jin kai, Sadiya Umar Farouq bisa tallafin tare da bayar da tabbacin za a raba kayayyakin ga wadanda suka dace.

 Mai magana da yawun tawagar da suka kai kayayyakin, Zeyed Mahmoud, ya ce sun dauki wannan mataki ne daga Sarkin Jordan domin tallafa wa wadanda ambaliyar ruwa ta shafa, kuma ya kasance tare da hadin gwiwar kasa da kasa da Nijeriya kan wannan iftila’i kasancewar kasashen biyu ‘yan uwan ​​juna ne.

Wakilinmu ya tattaro cewa babban daraktan hukumar ta NEMA ya samu hadin kai da wasu daraktocin hukumar wajen karbar tallafin.

Haka kuma a filin jirgin akwai jami’an hukumar Kwastam da hukumar shige da fice ta kasa (NIS) da sauran hukumomin da abin ya shafa.