Dalilin da ya sa aka zaɓi Qatar a matsayin wadda za ta karɓi baƙuncin kofin duniya

0
53

A shekara ta 2010 ne Qatar ta yi nasarar samun damar karɓar baƙuncin gasar kofin duniya bayan ta samu ƙuri’u 22 na shugabannin Fifa.

Ta yi nasara a kan Amurka, da Koriya ta kudu, da Japan, da kuma Australia, waɗanda su ma suka nemi karɓar baƙuncin gasar.

Ita ce ƙasar Larabawa ta farko da za ta ɗauki baƙuncin gasar.

An zargi Qatar da laifin bai wa jami’an Fifa cin hancin kuɗi dala miliyan 3 domin samun gyon bayansu, sai dai an wanke ta bayan wani bincike da aka gudanar na shekara biyu.

Shugaban Fifa na wancan lokaci Sepp Blatter ya nuna goyon bayansa ga Qatar a wancan lokacin, amma yanzu ya ce da alama Fifa din ta tafka kuskure.