Manchester united da Madrid na zawarcin Osimhen

0
69

Manchester United na shirin sayen dan wasan Napoli Victor Osimhen, dan Najeriya mai shekara 23, yayin da kungiyar ta Old Trafford ke neman dan gaba mai kai hari a kaka ta gaba.

Sai dai kuma kungiyar na fuskantar gogayya daga Real Madrid, inda Carlo Ancelotti ke kokarin shawo kan shugaban zakarun na Sifaniya Florentino Perez ya dauko Osimhen, da kuma dan AC Milan da Portugal Rafael Leao, a watan Janairu

Haka kuma Manchester United din na son sayen matashin dan wasan tsakiya na Benfica Enzo Fernandez, dan Argentina mai shekara 21.

Liverpool kuwa tana sha’awar matashin dan wasan Borussia Dortmund ne Youssoufa Moukoko, dan Jamus mai shekara 17, wanda ya ci kwallo shida a wasa 13 a bana.