Shugaba Buhari ya gana da sarki Charles III na Birtaniya a Landon

0
96

A yau ranar Laraba ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gana da mai martaba sarki Charles III a fadar Buckingham dake kasar Ingila.

In bamu manta ba, shugaba Buhari ya tafi Burtaniya hutun makwanni biyu ne sabida duba lafiyarsa a kasar.

Wannan dai shi ne karon farko da shugaban ya gana da sabon sarkin na Burtaniya kasancewar bai halarci bikin nadin sarautarsa ba da akayi a watan Oktoba.
LEADERSHIP ta ruwaito cewa mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ne ya wakilci shugaba Buhari a wajen taron.