Dan banga ya mutu har lahira yayin gwajin maganin bindiga a Taraba

0
55

Wani mutum mai suna Yusuf, wanda dan ’yan banga ne a karamar hukumar Jada a Jihar Taraba, ya rasa ransa yayin da abokin aikinsa Suugbomsumen Adamu, ya bindige shi a lokacin da yake kokarin gwada maganin bindiga.

Wata majiya ta bayyana cewa yaron mai shekaru 19 da a duniya, marigayin ya umuace shi da ya harbe shi bayan ya dana masa bindigar a cikinsa da nufin gwaji.

Kakakin rundunar ‘yansandan jihar, SP Suleiman Yahaya Nguroje, ya ce lamarin ya faru ne a ranar Alhamis.

Kakakin ya bayyana cewa rundunar za ta gurfanar da duk wanda aka samu na da hannu a lamarin.

Ya gargadi jama’a game da amfani da bindigogi yayin da ya shawarci masu dauke da su da su bi ka’idoji da dokokinsu don kare rayuwarsu da ta sauran jama’a.