Matakan da ake dauka don kauce wa karancin abinci a Najeriya – Ministar jin kai

0
42

Ambaliyar Ruwan da ta auku a daminar da ta gabata ta 2022 ta haifar da barna mai dimbin yawa a Nijeriya inda aka yi kiyasin cewa ta shafi akalla mutum miliyan uku da dubu dari biyu da shatara da dari bakwai da tamanin, inda sama da miliyan daya kuma suka rasa muhallansu baya ga gonakai sama da hekta dubu biyar da al’amarin ya shafa da sauran asarori daba-daban.

Yanzu haka dai ma’aikatar kula da al’amuran jin kai ta kasa ta dukufa rabon kayan tallafi ga wadanda abin ya shafa.

Ministar ta yi wa wakilinmu na fadar shugaban kasa, jonatan bayani a kan tallafin da ake yi da matakan da aka dauka na magance karincin abinci a Nijeriya sakamakon ambaliyar da kuma hanyoyin da ma’aikatar ke bi wajen ganin ba a maimaita handama da babakere na kayan tallafin ba kamar yadda aka gani lokacin rabon tallafin Korona.

Kamar yadda ka sani wannan ambaliya ta faru tsakanin wannan watan da ya wuce, watan Satumba da karshe zuwa Oktoba, kuma garuruwa da dama a fadin kasar nan wannan ambaliya ta shafe su, mun zo mun ba da bayani kan abin da gwamnatin tarayya ta yi na magancewa da ganin an kawo sassauci ga wannan abu da ya faru, saboda ambaliya ta zo wa mutane da yawa, jama’a sun rasa gonakinsu wasu ma sun rasa rayukansu, wasu kuma sun rasa hanyar cin abincinsu.

Gwanatin Tarayya a karkashin ma’aikatata ta ba da tallafin agaji ga wadanda abin ya shafa, wannan shi ne abin da muka zo muka fada muku masu yada labarai don ku san abin da muke yi a gwamnatance.