‘Yan sanda sun cafke dan damfara da katin cirar kudi 10 a Adamawa

0
52

Jami’an ‘yansandan Nijeriya a Jihar Adamawa sun kama wani matashi dan shekara 32 mai suna Joseph Nwakibe bisa zargin aikata damfara.

‘Yansandan sun ce sun kama wanda ake zargin dauke da katin cirar kudi (ATM) daban-daban har guda 10.

Rundunar ‘yansandan, a cikin wata sanarwa da kakakin ‘yansandan jihar, Suleiman Nguroje, ya sanya wa hannu, ta ce jami’an ‘yansanda sun yi ta sa ido a ranar Laraba, 8 ga watan Nuwamba, inda suka cafke matashin.

Rundunar ‘yansandan ta ce Joseph, dan asalin karamar hukumar Nnewi ta Kudu a Jihar Anambra da ke zaune a garin Markudi na Jihar Benuwe, an kama shi ne a wajen cirar kudi na bankin First Bank da ke Yola, babban birnin Jihar Adamawa.

Rundunar ‘yasandan ta kuma bayyana cewa abokinsa Obinna Ajima ne ya gayyace shi zuwa Yola domin gudanar da aikin damfara na hadin gwiwa.