Za mu ci gaba da sa ido kan Twitter – Gwamnati

0
52

Gwamnatin Najeriya ta ce tana ci gaba da sa ido kan kafar Twitter, duk da cewa ba ta da aniyar rufe wani dandalin sada zumunta.

Ministan Ministan Yada labarai da Raya Al’adu, Lai Mohammed ya bayyana haka ne a taron bayyana nasarori da ma’aikatun gwamnati daga shekarar 2015 zuwa 2023 da aka gudanar a Abuja a ranar Alhamis.

Ministan ya ce duk da cewa gwamnati ba ta da aniyar sake rufe wani dandalin sada zumunta, amma ba za ta bari a yi amfani da wani dandali ba wajen cin zarafi, da yada labaran kayar ko batanci ba.

Dangane da hakan ne ma ya ce suna sa ido kan Twitter, la’akari da yadda kamfanin ya sauya hannu, sabon shugaban kuma yake aiwatar da sauye-sauye a cikinsa.

“Sai da dandalin Twitter ya zama matattar masu son wargaza Najeriya ta hanyar yada labarun karya, kage, da kuma bantanci;  Babu kasar da za ta lamunce da wani dandali ya jefa ta ciki bala’i.

“Sai dai mun ci gaba da samun fahimtar juna da Facebook da Google da YouTube da kuma Twitter” in ji Ministan.

Yanzu kamfanin na Twiter ya zama mallakin attajri Elon Musk, wanda ya soma cinikinsa a watan Afrilu 2022, sannan ya kammala sayen sa tare da mallakarsa a ranar 27 ga watan Oktoba 2022.