Amurka ta ware Dala miliyan 50 domin tallafa wa Najeriya gudanar da zaben shugaban kasa a shekara maai zuwa.
Daga cikin abubuwan da za a yi da kudaden har da horas da ‘yan jarida da kungiyoyin fararen hula baya ga taimakawa wajen samar da kayayyakin aiki domin tabbatar da ingantaccen zabe.
Jakadan Amurka, Mista Will Stevens, shi ne ya sanar da tallafin a wannan Litinin a birnin Ibadan, babban birnin jihar Oyo a yayin wani taron horas da ‘yan jarida wanda Cibiyar Horas da Yada Labarai ta Yammacin Afrika WABMA ta shirya.
Mista Stevens ya ce, gwamnatin Amurka na aiki tukuru da aminanta ta hannun Hukumarta ta Raya Kasashe Masu Tasowa USIAD, domin ganin an kidaya kuri’ar kowa da kowa a yayiin zaben na 2023 a Najeriya.