HomeLabaraiMun yi wa ’yan Najeriya miliyan 65.5 rigakafin COVID-19 - Gwamnati

Mun yi wa ’yan Najeriya miliyan 65.5 rigakafin COVID-19 – Gwamnati

Date:

Related stories

INEC ta ce ba a kammala zabe a jihar Adamawa ba

Hukumar zaben Najeriya INEC, ta ayyana zaben gwamnan jihar...

An kashe ‘yan sanda 2, da dama sun raunata a wata arangama da sojoji a Taraba

A ranar Litin ne wasu sojoji suka kashe ‘yansanda...

Gwamna Zulum ya sake lashe zaben gwamna a jihar Borno

Sakamakon da hukumar zabe mai zaman kanta ta sanar...

Sojoji sun kashe hatsabinin dan ta’adda Umaru Nagona

Dakarun sojin Najeriya sun hallaka, Umaru Nagona, daya daga...

An kona gidan mawakin siyasa Rarara a Kano

Wasu da ake zargi ’yan daba ne sun banka...

Hukumar Kula da Lafiya a Matakin Farko ta Kasa (NPHCDA) ta ce an yi wa ’yan Najeriya kimanin miliyan 65.5 rigakafin COVID-19 daga watan Maris din 2021 zuwa yanzu.

Shugaban hukumar, Dokta Faisal Shu’aib, wanda ya shaida hakan a tattaunawarsa da Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ranar Lahadi a Abuja, ya kuma ce adadin alluran rigakafin da aka yi ya kai kusan miliyan 93.5.

Ya ce an fitar da alkaluman ne la’akari da yawan mutanen Najeriya da aka yi hasashe na shekarar 2022, wanda ya nuna cewa ’yan Najeriya miliyan 46.3 ne kacal ba a yi wa kowanne irin nau’in rigakafin ba.

Dokta Faisal ya kuma ce jihar Adamawa ta shiga sahun jihohi 12 da suka sami nasarar yi wa sama da rabin ’yan jiharsu rigakafin cutar ta COVID-19 a Najeriya.

Shugaban ya kuma ce rigakafin samfurin Johnson and Johnson wacce aka kawo Najeriya a watan Fabrairun 2022 ita ce aka yi wa kimanin kaso 60 cikin 100 na mutanen da aka yi wa ita.

Ya kuma ce jihohi biyar da ke kan gaba wajen yawan yi wa mutanensu rigakafin cutar a kasar sun hada da Nasarawa da Jigawa da Osun da Kaduna da kuma Kano.

Kazalika, ya ce su ma jihohin Osun da Kaduna da Kebbi da kuma Sakkwato sun yi wa kusan rabin mutanensu rigakafin daga lokacin da aka farab yin ta ya zuwa yanzu.

“Jihohi uku da ke kan gaba wajen yawan yi wa mutane rigakafin su ne Kaduna (miliyan 3.3) da Kano (miliyan 2.8) da Osun (miliyan biyu da rabi) kowaccensu,” inji Dokta Faisal

Ya ce an fitar da alkaluman ne la’akari da yawan mutanen Najeriya da aka yi hasashe na shekarar 2022, wanda ya nuna cewa ’yan Najeriya miliyan 46.3 ne kacal ba a yi wa kowanne irin nau’in rigakafin ba.

Dokta Faisal ya kuma ce jihar Adamawa ta shiga sahun jihohi 12 da suka sami nasarar yi wa sama da rabin ’yan jiharsu rigakafin cutar ta COVID-19 a Najeriya.

Shugaban ya kuma ce rigakafin samfurin Johnson and Johnson wacce aka kawo Najeriya a watan Fabrairun 2022 ita ce aka yi wa kimanin kaso 60 cikin 100 na mutanen da aka yi wa ita.

Ya kuma ce jihohi biyar da ke kan gaba wajen yawan yi wa mutanensu rigakafin cutar a kasar sun hada da Nasarawa da Jigawa da Osun da Kaduna da kuma Kano.

Kazalika, ya ce su ma jihohin Osun da Kaduna da Kebbi da kuma Sakkwato sun yi wa kusan rabin mutanensu rigakafin daga lokacin da aka farab yin ta ya zuwa yanzu.

“Jihohi uku da ke kan gaba wajen yawan yi wa mutane rigakafin su ne Kaduna (miliyan 3.3) da Kano (miliyan 2.8) da Osun (miliyan biyu da rabi) kowaccensu,” inji Dokta Faisal.

Subscribe

- Never miss a story with notifications

- Gain full access to our premium content

- Browse free from up to 5 devices at once

Latest stories