Sheikh Dahiru Bauchi ya halarci wa’azin da kungiyar Izala ta gudanar a Bauchi

0
64

Sheikh Ibrahim Dahiru Usman Bauchi, ya halarci wa’azin da kungiyar Izala ta gudanar a ranar Asabar a garin Misau dake jihar Bauchi.

Shugaban kungiyar na kasa Sheikh Abdullahi Bala Lau ne ya jagoranci wa’azin tare da  sakataren kungiyar Izala na kasa Sheikh Dr. Muhammad Kabiru Haruna Gombe da sauran manyan jiga-jigan kungiyar Izala.

Sheikh Ibrahim Dahiru usman Bauchi ya wakilci sarkin musulmi ne a wajen wa’azin, an gudanar da wa’azin ne daren jiya Asabar a kofar mai martaba sarkin Misau.

Na tabbata dubbannin musulmaine za suyi farin cikin ganin ana samun hadin kai a tsakanin jagororin bangarori na musulmi a Najeriya.

Allah ya taimaki shuwagabannin mu ya kara musu hadin kai, ya kara dorasu akan daidai.