Dan majalisar da ya yanke jiki a taron kaddamar da yakin neman zaben Tinubu ya rasu

0
187
Dan Majalisar Dokokin Jihar Legas mai wakiltar mazabar Mushin II, Sobur Olayiwola Olawale ya rasu.

Olawale wanda aka fi sani da Omititi, na cikin ‘yan siyasar da suka halarci taron kaddamar da yakin neman zaben dan takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Tinubu a Jos, babban birnin Jihar Filato.

Rahotanni sun bayyana cewa marigayin ya yanke jiki ya fadi a wajen taron kuma daga bisani ya ce ga garinku nan.

Wani jigo a jam’iyyar APC da ya nemi a sakaya sunansa ya shaida wa Aminiya cewa ko a karshen makon da ya gabata suna tare da Olawale.

“Mun hadu ne a gidan Sanata Ganiyu Olanrewaju Solomon (GOS) a ranar Lahadi, inda muka gaisa. Kuma a wancan lokacin yana cikin koshin lafiya.

“Koma mene ne amma da alamu mutuwarsa na da alaka da hawan jini. Amma mutuwarsa ta girgiza mu.