ASUU: Gwamnati ta kafe kan kudurinta a kan malaman jami’o’i na ba aiki ba biyan albashi

0
58

Gwamnatin tarayya ta sake nanata kudirinta kan kungiyar malaman Jami’o’i (ASUU) na matakin da ta dauka, ‘Ba Aiki Babu Albashi’.

Ministan Ilimi, Malam Adamu Adamu ne ya jaddada matsayar gwamnatin tarayya dangane da zanga-zangar da kungiyar ta ASUU ta yi kwanan nan kan biyan ‘ya’yanta rabin albashi.

Ya bayyana hakan ne yayin da yake amsa tambayar manema labarai na fadar shugaban kasa jim kadan bayan kammala taron mako-mako na majalisar zartarwa ta tarayya (FEC), wanda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jagoranta, a fadar shugaban kasa a Villa, Abuja.

Ya ce, “Kungiyar Malaman ta janye yajin aikin kuma gwamnati ta biya su abin da ya kamata. Ina ganin matsayin gwamnati ke nan; cewa ba za ta biya kowa kudin aikin da bai yi ba, ina tsammanin gwamnati ta biya su kudin adadin kwanakin da suka yi na aiki.