Malaman jami’ar Bayero sun yi zanga-zanga kan albashi

0
58

Kungiyar malaman jami’o’in Najeriya ASUU reshen jami’ar Bayero da ke Kano ta gudanar da zanga-zangar lumana ta rana guda domin nuna bacin rai dangane da abin da ta kira rashin cika alkawari daga bangaren gwamnati wadda ta ce, ba za ta biya su albashi ba.

Kungiyar ta ce dukkan jami’o’i bakwai da ke wannan shiyya sun shiga  zanga-zangar, domin gabatar da kokensu ga shugabannin jami’o’in.

Gwamnatin ta ce, ba za ta biya malaman albashin ba da su yi aikinsa ba kamar yadda Ministan Ilimin Kasar, Adamau Adamu ya bayyana.

Tun a cikin watan Fabairun da ya gabata ne, kungiyar ta ASUU ta tsunduma yajin aiki, yayin da ta janye a cikin watan Oktobba bayan kakakin majalisar wakilan kasar, Femi Gbajabiamila ya shiga tsakanin bangarorin biyu.

Sai dai malaman na jami’a sun karbi rabin albashinsu ne a karshen wtan Oktoba, matakin da malaman suka ki amincewa da shi.

Ministan ya nanata cewaa, matsayar gwamnatin kasar, ita ce, ba za ta biya wannan albashin ba.