’Yan bindiga sun kashe mutum 9 ’yan gida daya a Filato

0
117

’Yan bindiga sun kashe wasu mutum tara ’yan gida daya a kauyen Maikatako da ke Karamar Hukumar Bokkos ta Jihar Filato.

Kakakin rundunar ’yan sandan Jihar Filato, Mista Alfred Alabo, ya tabbatar da faruwar lamarin yayin taron manema labarai a ranar Laraba.

Alabo ya ce ’yan bindigar da suka afka wa kauyen a daren Talata kai tsaye suka shiga harbi kan mai uwa da wabi.

Kakakin ’yan sandan wanda ya ce tuni bincike ya kankama kan faruwar lamarin, ya kuma sha alwashin yi wa manema labarai karin haske a nan gaba kadan.

Wani mazaunin kauyen da zanta da Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya NAN, ya ce zuwa yanzu dai sun tsinto gawarwakin mutum 18 kuma suna ci gaba da lalube.

A cewarsa, akwai fargaba a tsakanin al’ummar duk da kasancewar jam’ian tsaro da suka hada da ’yan sanda da sojoji da ke ci gaba da sintiri.