An yi wa fursunoni 176 afuwa a Ribas

0
100

Anyi hahan ne a matsayin wani mataki na rage cunkoso a babban gidan gyaran hali da ke Fatakwal, babban birnin Jihar Ribas, an yi wa fursunoni 176 masu kananan laifuka afuwa.

Matakin wanda aka dauka ta bangaren shari’ar jihar, an saki fursunonin ne ba tare da gindaya musu wani shardi ba.

Mai magana da yawun Hukumar Kula da Gidajen Gyaran Hali (NCoS) a Jihar ta Ribasa, DSC Juliet Ofoni, ita ce ta bayyana haka a ranar Talata.

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya rawaito cewa, afuwar na zuwa ne a daidai lokacin da jihar ke wani biki da ya shafi bangaren shari’ar jihar.

Alkalin-Alkalan jihar, Simeon Amadi, ya yaba wa Konturolan Hukumar Kula da Gidajen Gyaran Hali a jihar, Mista Felix Lawrence da kuma jami’i mai kula da Babbar Cibiyar Tsaro da ke Fatakwal, Mista Efiong Okon Etim bisa kokarin da suke yi dangane da aikinsu.

Alkalin ya yi amfani da wannan damar wajen kira ga fursunonin da aka yi wa afuwar da su kasance ‘yan kasa nagari, sannan su guji aikita duk wani laifi da zai sa su koma gidan jiya.