Sake fasalin Naira: Adadin gwamnonin da EFCC ke bibiya na sake karuwa – Bawa

0
59

Shugaban Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (EFCC), Abdulrasheed Bawa, ya ce adadin gwamnonin da ke cikin jerin sunayen da hukumar ke bibiya su kan iya karkatar da kudade, saboda shirin sake fasalin Naira.

Ya bayyana hakan ne ga manema labarai a fadar shugaban kasa a ranar Alhamis bayan ya gana da shugaban kasa Muhammadu Buhari a fadar shugaban kasa da ke Abuja.

Sai dai ya ki bayar da takamaiman adadin wadanda hukumar ke bibiya.

Idan dai za a iya tunawa, makonni biyu da suka gabata, Bawa ya yi tsokaci kan ayyukan sa ido da hukumar EFCC ke yi wa wasu gwamnoni uku, kan zarginsu da alamun karkatar da kudaden jama’a, biyo bayan sanarwar da gwamnatin tarayya ta yi na sake fasalin Naira.