Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa mutane miliyan 133 a Najeriya, wanda ya nuna kashi 63 cikin 100 na fama da talauci.
An gabatar da wannan adadi ne yayin da ake kaddamar da bincike kan Talauci na Nijeriya (MPI) a Abuja a yau Alhamis.
Hukumar Kididdiga ta Kasa (NBS), Ofishin Kula da walwalar ƴan ƙasa da kasa (NASSCO), Hukumar Bunkasa Ci Gaban Majalisar Dinkin Duniya (UNDP), Asusun Yara na Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF), da kuma Oxford Poverty and Human Development ne suka gudanar da shirin.
Daily Trust ta ruwaito cewa, matakin da aka yi amfani da shi wajen kididdige wannan adadi ya samo asali ne a kan Ma’aunin Talauci Daban-daban (MPI) da ke da bangarori biyar na kiwon lafiya, da rayuwa, da ilimi, da tsaro da kuma rashin aikin yi.
Binciken, wanda ya yi misali da gidaje sama da 56,000 a fadin Jihohi 36 na Tarayya da Babban Birnin Tarayya Abuja, wanda aka gudanar tsakanin watan Nuwamba 2021 zuwa Fabrairu 2022, ya nuna cewa kashi 65 cikin 100 na talakawa, miliyan 86, suna zaune ne a Arewa, yayin da kashi 35, kusan kusan Miliyan 47 suna zaune a Kudu.
Ya bayyana jihar Sokoto a matsayin tafi kowacce jiha yawan talauci a fadin Jihohin kasar, inda take da kashi 91 cikin dari yayin da Ondo ke da kaso 27 cikin dari.
Da yake jawabi a wajen taron, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce an dauki matakin ne domin samar da hanyoyin da za a iya gano talauci da kuma tinkarar manufofin magance shi.
Buhari ya samu wakilcin shugaban ma’aikatan fadar sa Farfesa Ibrahim Gambari.
Rahoton ya kara da cewa, “sama da rabin al’ummar Najeriya talakawa ne masu yawan gaske kuma suna yin girki da taki, itace ko gawayi, maimakon makamashi mai tsafta. Babban rashi kuma yana bayyana a cikin ƙasa a cikin tsafta, lokacin kiwon lafiya, rashin abinci, da gidaje. ”
“Gaba ɗaya, yawan talaucin kuɗi ya yi ƙasa da yawan talaucin da ake fama da shi a yawancin jihohi. A Najeriya, kashi 40.1% na mutane matalauta ne bisa ga tsarin talauci na kasa na shekarar 2018/19, kuma kashi 63% na fama da talauci da yawa, a cewar MPI 2022.”