An kashe wata ’yar aiki da duka a Filato

0
61

Wata ’yar aiki ta riga mu gidan gaskiya sakamakon dukan da iyayen gidanta da suka lakada mata.

An tabbatar da mutuwar yarinyar mai suna Margaret ne a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Jos.

Rahotanni sun ce, Margaret ta mutu ne sakamakon raunukan da ta ji a dalilin dukan da ta ci a hannun ma’auratan da take yi wa a iki a yankin Vom, cikin Karamar Hukumar Jos ta Kudu.

An ce rashin kula da raunukan da marigayiyar ta ji ya sa kwayoyin cuta suka samu shiga cikinta tare da yin ajalinta.

Ana zargin cewa, ba yau ne farau ba, wadanda ake zargi da kashe yarinyar sun saba gana mata azaba.

Hukumar Kula da Hakkin Dan Adam ta Kasa (NHRC) a Jihar Filato, ta tabbatar da aukuwar lamarin.

Hukumar ta ce ta gano an yiwo safarar marigayiyar daga Jihar Kebbi ne sannan aka damka ta ga wadanda take yi wa aiki.

Mai magana da yawun ’yan sandan jihar, DSP Alfred Alabo, ya ce an damke matar da ake zargi da hannu cikin mutuwar yarinyar an kuma fara bincike kafin daga bisani a gurfanar da ita a kotu.