Masu cutar sikari na fuskantar karin kudin magani da kashi 200

0
74

‘Yan Nijeriya wadanda suke fama da cutar Sikari sun yi kira ga gwamnatin tarayya da cewar ta cire harajin da ake biya na magunguna,da sauran kayan gwaji na cutar Sikari saboda yadda farashin magungunan ya karu ya kara sa wadanda suke fama da  cutar cikin mawuyacin hali na rayuwa.

Binciken da jaridar LEADERSHIP ta gudanar ya nuna mai fama da cutar Sikari a Nijeriya yana kashe Naira dubu talatin (#30,000) kowanne wata a wannan shekara ta muke ciki ta 2022, wannan kudin magani ne da kuma gwaji,wanda idan aka tuna a baya shekarar 2019 kudin Naira dubu goma ne (#10,000) ake biya.

Duk wannan ma baa bin damuwa bane matsaslar ita ce shi maganin insulin da kwararru na cutar Sikari (endocrinologist), ba samun shi ake cikin sauki ba,yayiin da su kwararrun basu da yawa.Irin hakan ke kara sa masu fama da cutar shiga wani halin kaka- nika yi.