An kama wani likitan bogi a Neja

0
64

Rundunar ‘yan sandan jihar Neja ta samu nasarar kama wani mutum mai suna Clement Joseph da ke garin Koropka, karamar hukumar Chanchaga, wanda yake bayyana kansa a matsayin likita.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar DSP Wasiu Abiodun, ya sanar da manema labarai a garin Minna.

Ya ce, sun kama likitan bogin kan wasu laifuka guda uku da ake zarginsa da aikata wa.

Ya ce, “An kama wanda ake zargin da laifin yin karyar cewa, shi likita ne ya kuma karbi kudi a hannun wani mutum da sunan zai yi masa magani”.

Abiodun ya ce, kokacin da ake yi masa tambayoyi, ya tabbatar da cewa, shi ba likita ba ne.

 A karshe dai, za a ci gaba da bincike domin tabbatar da gaskiyar abin da ya faru, wanda kuma idan laifin da ake zarginsa da shi ya tabbata zai gurfana gaban kitu, domin yi masa gukunci.