Wizkid ya lashe kyautar AMA a Amurka

0
135

Fitaccen mawakin  da ya shahara a salon wakar Afrobeat, Ayodeji Ibrahim Balogun da aka fi sani da Wizkid da kuma takwararsa ta kasar, Temilade Opaniyi da aka fi sani da Tems, sun sake daga martabar kasar a Iadon duniya, inda suka lashe lambar yabo ta AMA a Amurka.

Wikzid ya kafa tarihi bayan ya doke Burna Boy da Ckay da Tems da Fireboy, inda ya zama mutun na farko da ya lashe kyautar a bangaren mawakan afrobeat a bana.

Tems ta yi nasara ce bayan an zabe ta a matsayin wadda ta fi nuna hakaza a bana a bangaren salon wakar R&B.

A karon farko kenan da Wizkid ke lashe wannan kyauta  bayan da sau uku yana takarar lashe ta amma bai samu nasara ba, sai a bana.

A karo na 50 kenan da ake gudanar da bikin na AMA wanda  aka gudanar a dakin taro na Microsoft Theatre da ke Los Angeles a Amurka a jiya Lahadi wanda sharararren mai gabatar da shirin talabijin Wayne Brady ya  jagoranta.

Kyautar AMA dai, ita ce mafi girma a duniya wadda magoya baya ke zaben tauraronsu.