Amfani biyar game da samun man fetur a Arewacin Najeriya

0
46

A ranar Talata shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ƙaddamar da aikin haƙo man fetur a yankin Kolmani da ke tsakanin jihohin Bauchi da Gombe.

A shekarar 2019 ne dai kamfanin mai na ƙasar NNPC ya bayyana gano tarin arzikin albarkatun man fetur a yankin na Kolmani da ke kan iyakar Bauchi da Gombe da ke yankin arewa maso gabashin Najeriya.

Shugaba Buhari ya ce yankin Kolmani na da arzikin albarkatun man fetur da ya kai ganga biliyan ɗaya da kuma kyubik biliyan 500 na iskar gas.

Shugaban ƙasar ya faɗa a wajen taron cewa an samu masu zuba waɗanda suka zuba jarin da ya kai dala biliyan uku domin aikin haƙo man na Kolmani.

Haka kuma shugaban ƙasar ya umarci kamfanin mai na NNPC tare da abokan aikinsa da su yi aiki tare da mazauna yankin tare da kiran da su koyi darasi daga abin da ke faruwa a yankin Niger Delta , inda ‘yan bindiga ke fasa bututun mai, bayan da suka zargi kamfanonin da ke haƙo man a yankin da yin watsi da su.

Shugaban ƙasar ya ce ya tattauna da gwamnonin Bauchi da Gombe, inda suka tabbatar masa cewa za su bayar da haɗin kai domin ci gaba da aikin bunƙasa haƙo man fetur ɗin.

BBC ta tattauna da ɗaya daga cikin manyan jami’an kamfanin mai na NNPC da ke kula da inda kamfanin ke zuba jari, Bala Wunti, inda ya shaida wa BBC cewa ana fatan gina matatar mai da kamfanonin samar da taki da kuma iskar gas.