HomeLabaraiMagoya bayan Rasha sun kai hari kan shafin EU

Magoya bayan Rasha sun kai hari kan shafin EU

Date:

Related stories

Abba gida-gida ya lashe zaben gwamnan Kano

Hukumar Zabe ta Kasa, INEC ta sanar da cewa...

INEC na neman ta ce zaben gwamnan Kano ‘Inconclusive’ ne — Kwankwaso

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NNPP, sanata Rabiu...

Zaben gwamnan Kano: Ratar kuri’ar da ke tsakanin NNPP da APC

Bayan bayyana sakamakon kananan hukumomi 44 na zaben gwamnan...

Jami’in tattara sakamakon zabe ya yanke jiki ya fadi a hedikwatar INEC a Kano

Jami’in tattara sakamakon zabe, Farfesa Muhammad Yushau na karamar...

Sakamakon zaben gwamnonin jihohin Najeriya

Wannan shafin zai rika kawo muku kammalallen sakamakon zaben...

An kaddamar da hari kan shafin yanar gizo na majalisar dokokin kungiyar kasashen Turai, lamarin da ke zuwa jim kadan da ‘yan majalisar suka amince da wani kudirin doka da ke ayyana Rasha a matsayin kasar da ke daukar nauyin ta’addanci.

Shugabar majalisar tarayyar Turai, Roberta Metsola ta ce, an kai gagarumin farmakin intanet kan majalisar kuma wata kungiya da ke goyon bayan gwamnatin Rasha ta dauki alhakin harin.

Metsola ta ce, tuni kwararrunsu masana yanar gizo suka fara dakile harin tare da bai wa shafin majalisar kariya, yayin da ta jaddada goyon bayanta ga Ukraine.

Wata majiya daga majalisar wadda ta bukaaci a sakaya sunanta ta ce, wannan harin shi ne mafi muni da aka kai wa shafin majalisar a tarihi.

Shafin dai ya durkushe ne jim kadan da ‘yan majalisar tarayyar Turan suka kada kuri’ar amincewa da Rasha a matsayin kasar da ke tallafa wa ayyukan ta’addanci sakamakon hare-harenta a Ukraine.

Kungiyar Killnet wadda ta dauki alhakin kai harin na yanar gizo, a can baya, ta taba cewa, ita ce ta kai farmaki kan shafukan intanet na Amurka, sannan kuma tana yi wa wasu kasashen da ke adawa da mamayar Rasha a Ukraine barazana.

Tuni shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky ya yi lale marhabin da matakin ayyana Rasha a matsayin mai daukar nauyin ta’addanci.

Subscribe

- Never miss a story with notifications

- Gain full access to our premium content

- Browse free from up to 5 devices at once

Latest stories