Magoya bayan Rasha sun kai hari kan shafin EU

0
59

An kaddamar da hari kan shafin yanar gizo na majalisar dokokin kungiyar kasashen Turai, lamarin da ke zuwa jim kadan da ‘yan majalisar suka amince da wani kudirin doka da ke ayyana Rasha a matsayin kasar da ke daukar nauyin ta’addanci.

Shugabar majalisar tarayyar Turai, Roberta Metsola ta ce, an kai gagarumin farmakin intanet kan majalisar kuma wata kungiya da ke goyon bayan gwamnatin Rasha ta dauki alhakin harin.

Metsola ta ce, tuni kwararrunsu masana yanar gizo suka fara dakile harin tare da bai wa shafin majalisar kariya, yayin da ta jaddada goyon bayanta ga Ukraine.

Wata majiya daga majalisar wadda ta bukaaci a sakaya sunanta ta ce, wannan harin shi ne mafi muni da aka kai wa shafin majalisar a tarihi.

Shafin dai ya durkushe ne jim kadan da ‘yan majalisar tarayyar Turan suka kada kuri’ar amincewa da Rasha a matsayin kasar da ke tallafa wa ayyukan ta’addanci sakamakon hare-harenta a Ukraine.

Kungiyar Killnet wadda ta dauki alhakin kai harin na yanar gizo, a can baya, ta taba cewa, ita ce ta kai farmaki kan shafukan intanet na Amurka, sannan kuma tana yi wa wasu kasashen da ke adawa da mamayar Rasha a Ukraine barazana.

Tuni shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky ya yi lale marhabin da matakin ayyana Rasha a matsayin mai daukar nauyin ta’addanci.