‘Yan bindiga sun sace fiye da mutum 100 a Zamfara

0
114
Sama da mutane 100 ne aka tabbatar da cewa wasu ’yan bindiga sun yi garkuwa da su a Jihar Zamfara da ke Arewa maso Yammacin Najeriya.

Gidan Rediyon Jamus DW ya ruwaito cewa, wasu dauke da bindigogi sun shiga kauyuka hudu na Jihar Zamfara, inda suka kwashi mutanen da suka hada da mata da kuma kananan yara.

Fiye da mutum 40 aka kwashe daga kauyen Kanwa na Karamar Hukumar Zurmi, yayin da wasu 37 din su ma aka kwashe su daga kauyen Kwabre, a cewar Kwamishinan Watsa Labarai na Jihar Zamfara, Malam Ibrahim Dosara.

Haka ma a cewar Malam Dosara, an kwashi wasu mutane akalla 38 a kauyukan ’Yankaba da Gidan-Goga da ke Karamar Hukumar Maradun.

Garkuwa da mutane domin neman kudin fansa a Arewacin Najeriya dai, ta zama wata gagarumar matsalar da ke faruwa ba dare da rana, kama daga cikin gonaki zuwa kan hanyoyi na manyan da kananan garuruwa.