HomeLabaraiGobara ta tashi a tashar mota ta NTA da ke Filato

Gobara ta tashi a tashar mota ta NTA da ke Filato

Date:

Related stories

INEC ta ayyana 29 ga Maris a matsayin ranar zaben cike gurbi a Adamawa

Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC), ta...

IPOB ta umarci ‘yan kabilar Igbo da ke Legas su koma gida

Kungiyar masu rajin kafa ā€˜yantacciyar kasar Biafara ta IPOB,...

Sarkin Kano ya taya Abba Kabir murnar lashe zaben gwamnan Kano

Sarkin Kano Aminu Ado Bayero ya taya Abba Kabir...

Mata magoya bayan PDP na zanga-zangar kin amincewa da zabe a Kaduna

Wata tawagar mata sanye da bakaken kaya na jam’iyyar...

Gobara ta kone fitacciyar tashar mota ta NTA da ke garin Jos, babban birnin Jihar Filato.

Mista Matthew Edogbonya, kakakin Hukumar Kashe Gobara ta Tarayya a Jihar Filato, bai samu damar amsa waya ba.

Amma wani babban jami’in hukumar da ya bukaci a sakaya sunansa, ya tabbatar wa Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) da faruwar lamarin a Jos.

ā€œKakaki da sauran manyan jami’an hukumarmu suna wurin da gobarar ta tashi sai dai har yanzu ba su ce komai ba.

ā€œBa za mu iya cewa ga musabbabin faruwar gobarar ba, amma an tura mutanenmu wurin domin kashe ta.

ā€œA halin yanzu, ba za mu iya cewa ga adadin abubuwan da suka salwanta ba.

ā€œAbin da muka fi damuwa da shi a yanzu shi ne kashe gobarar saboda kada ta lalata dukiya ko salwantar rayukan mutane,ā€ in ji shi.

NAN ta ruwaito cewa tashar motar na daura da gidan talabijin na NTA da ke Jos, wanda ke kan hanyar Yakubu Gowon, Jos.

Subscribe

- Never miss a story with notifications

- Gain full access to our premium content

- Browse free from up to 5 devices at once

Latest stories