Likitoci 199 daga cikin 280 da muke biyan albashi na bogi ne – Matawalle

0
85

Gwamnan Jihar Zamfara, Muhammad Bello Matawalle, ya ce gwamnatinsa ta gano sunayen likitocin bogi kimanin 199, wadanda ake biyan albashi a jihar.

Gwamna Matawalle na wannan jawabi ne a wani taron manema labarai a gidansa da ke Karamar Hukumar Maradun.

Matakin na zuwa ne a dai-dai lokacin da ake kokawa game da tsaikon da aka samu wajen biyan albashi ma’aikatan lafiyar jihar, lamarin da Gwamna Matawalle ya ce cuwa-cuwar da suka bankado ce sila amma tuni sun sauke nauyin duk wani albashi na watannin Nuwamba da Disamba.

A cewar gwamnan yayin da gwamnatin jihar ke biyan likitoci 280 albashi a jihar a duk wata, ta gano cewa likitoci 81 ne kawai ke aiki a jihar.

“Muna biyan albashin likitoci 280 amma mun gano cewa likitoci 81 kacal ne na hakika.”

Gwamnan ya kara da cewa tuni ya zanta da Kungiyar Kwadago ta Kasa (NLC) domin gano wadannan likitoci 199, da suka kwashe tsawon lokaci suna karbar albashi alhalin ba sa yi wa gwamnatin jihar aiki.

Ya kuma ce akwai bukatar a gano wadanda ke da hannu a wannan cuwa-cuwa.

Matawalle ya ce an gano wadannan sunaye ne sakamakon aikin tantance ma’aikata da gwamnatin jihar ke gudanarwa karkashin Ofishin Shugaban Ma’aikata na jihar, a wani bangare na kokarin da gwamnatin ke yi na fara aiwatar da tsarin biyan albashi mafi karanci na N30,000.