Cutar sarkewar numfashi ta kashe Mutane 25 a jihar Kano

0
118

Kamfanin labarai na SOLACEBASE ya rahoto cewa cutar nan mai kashe kananan yara da aka fara gano ta a Kano a karshen shekarar da ta gabata, ta barke, yanzu haka ana kula da majinyata da dama wasu kuma sun rasu a Asibitin kwararru na Murtala Muhammed da Asibitin Koyarwa na Aminu Kano, AKTH, da ke jihar.

Kwararrun likitocin sun ce, cutar diphtheria cuta ce mai tsanani ta hanci da makogwaro da ake iya yin rigakafinta ta hanyar bayar da magunguna.

A cewar masana, alamun cutar ta shakewar numfashi (diphtheria) sun hada da: bushewar makogwaro da mawuyaciyar fitar numfashi ko fitar numfashi cikin sauri-sauri da zubar majina da zazzabi da saurin jin gajiya.

Jaridar ta gano cewa an fara samun cutar ne daga karamar hukumar Ungogo da ke Kano.

A cewar bayanan ma’aikatar lafiya ta jihar Kano da SOLACEBASE ta samu, Mutane 58 ne ake zargin sun kamu da cutar, 6 an kwantar da su sannan kuma 25 sun mutu sakamakon kamuwa da cutar diphtheria a ranar 13 ga Janairu, 2023.