Ya kamata gwamnonin arewa su dinga koyi da yadda Zulum yake mulkinsa – Abdullahi Radda

0
82
Abdullahi Bala Radda
Abdullahi Bala Radda

FAGEN SIYASA – HAUSA24

A shirin mu na Fagen Siyasa na wannan makon munyi katari da matashin dan siyasa Abdullahi Bala Radda inda muka zanta dashi akan al amuran siyasa.

Radda ya bayyana mana yadda ya tsinci kansa acikin harkar siyasa inda yace gwamna Babagana Umara Zulum shine jigon da yake kallo, kuma shi ya ja ra’ayinsa akan harkar siyasa duk da shi yaro ne me kananun shekaru.

Ya shaida mana cewa irin soyayyar da yake wa Zulum bata da iyaka ballantana ma ta fadu, dalilin wannan kauna har zuwa yayi bankunan sa saboda a gyaramai sunayensa a saka mai Zulum acikin sunayen da yake amfani dasu.

“Allah ne ya hada jinina da Zulum, bai sanni ba haka zalika ni ko hanyar zuwa Borno ban sani ba. Ni dan asalin jihar Katsina ne ba dan Borno ba amma irin kyawawan ayyukan da gwamna Zulum yake yiwa jiharsa ta Borno da kuma yadda yake kaunar matasa ta sa naji ina kaunar sa” inji Radda.

Ya kara da cewa “in gwamnonin arewa zasu dinga koyi da irin ayyukan alkhairi da ya keyi a jihar sa to yan arewa na ko wace jiha zasu ji dadin mulkin demokoradiya”

“Zulum mutum ne me jinkan talakawa, mun san halin da jihar Borno take a da amma zuwan sa yau jihar Borno ta zauna kalau abubuwa da yawa sun canza matasa da basu da sana’a ana ya samar musu abin yi. Su matasa in aka taimake su hakan yana kawo cigaba a gari sosai, saboda zaka hanasu zaman banza sannan zaka kawar dasu daga fadawa wani irin hali duba da yadda shaye-shaye ya yawaita ta ko ina. Toh Zulum yana da taimakon matasa ta wannan bangaren wanda wasu jihohin zakaga akasin hakan ne”

“Da haka nake cewa ya kamata gwamnonin mu na sauran jihohi na arewa harda ma na sauran jihohin kudu da su dinga koyi da irin ayyukan da yakeyi, da kuma yadda yake gudanar da mulkinsa”

“A karshe ina kira da matasa, wannan zaben da yake tunkaro mu nan da kwanaki kadan da ku tsaya ku zabi mutanen kwarai wanda zasu taimaki rayuwarku dama al’uma gaba  daya rayuwa kullum kara tsananta take amma inda shugabanni na gari komai zai dinga zuwa da sauki.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here