An yaudare mu a kan kwangilar P&ID ta iskar gas

0
224

Najeriya ta shaida wa Babbar Kotun Birnin London cewa, an yaudare ta ne a wata kwangilar iskar gas tsakaninta da Kamfanin P&ID, inda a yanzu ta bukaci kotun da ta janye hukuncin da ta yanke mata na biyan Dala biliyan 11 ga wannan kamfanin.

Tun a watan Janairun 2019, aka kulla wannan harkallar mai cike da badakala, lokacin da kamfanin na P&ID ya rattaba hannu kan yarjejeniyar jigilar iskar gas da sarrafa ta tare da Ma’aikatar Albarkatun Man Fetur a madadin gwamnatin Najeriyar.

Karkashin yarjejeniyar dai, bangarorin biyu sun amince cewa, kamfanin na P&ID zai gina tare da habbaka aikin samar da iskar gas a Karamar Hukumar Odukpani ta jihar Cross Rivers, inda kuma ita Najeriya za ta tatso iskar gas din daga wasu wuraren hakar danyen mai domin amfani da ita wajen samar da wutar lantarki a kasar.

Sai dai jim kadan da kulla yarjejeniyar, kamfanin na P&ID ya yi zargin cewa, Najeriya ta karya alkawarinta ta fuskar samar da filin da za a gudanar da aikin iskar gas din, lamarin da ya sukurkuta kwangilar, Wanda hakan ya hana kamfanin samun riba.

Ita ma dai Najeriyar ta zargi kamfanin da karya wani bangare na yarjejeniyar, yayin da bangarorin biyu dunguma zuwa wata kotun kasuwanci a Birtaniya bayan sasanci a tsakaninsu ya ci tura a Najeriya.

Bayan Najeriya ta gaza samun nasara, kotun dai ta umarci gwamnatin kasar da ta biya diyya ga  kamfanin, yayin da a yanzu, kudin ruwan diyyar ya zarta Dala biliyan 11, kwatankwacin kashi 30 na asusun ajiyar kudaden ketare na kasar.

A makon ne aka ci gaba da zaman kotun, amma Najeriya ta gabatar da wani sabon korafi tana mai cewa, an ma yaudare ta ne a wannan kwangilar ta iskar gas, sannan kuma P&ID ya bayar da cin hanci da wasu jami’an kasar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here