Rashin dacewar koya wa ‘ya’ya taya uwa kishi

0
58

Iyaye mata kan rasa tunaninsu a yayin da bakin kishi ya lullbe mu su zuciya babu abin da su ke tunawa ban da duk wata hanyar da za su bi wajen cusgunawa amarya.

Dan haka yanzu nasihar Uwa ga yaranta ta tashi daga kan su yi ladabi da biyayya ga  na gaba da su, ta koma kan yadda za su yi rashin kunya da sharri da hada tuggu ga amarya don  kori ta.

Wannan hali ya fi tasiri a kan ‘yaya mata fiye da ‘ya’ya  maza, wasu yaran maza su na daukar muguwar shawarar da uwa ta ke ba su a lokacin da su ke  da karancin shekarun amma da yawan yara maza idan sun fara girma ba su cika biyewa uwa ba, su kan ba ta shawara ma a kan ta daina damuwa.

Amma yara mata da ya ke a koda yaushe su na zaune ne a gida su na ara su yafa wajen taya mahaifiyarsu kishi har ma fi ta jin zafi da haushin amaryar.

Sai Uwa ta koma gefe ta na jin dadi ta na cewa ba da ni za ta yi kishi ba na bar ta da yara.

Amarya ta na shiga tashin hankali da rashin sukuni da zarar an ce maigida zai fita sai gabanta ya yi ta faduwa don zai tafi ya bar ta da yaran gidan, don ba za su iya yi mata komai a gabansa ba saboda su na tsoro kuma ba za su bari ya ga wata alama ba a gabansa don haka ko amarya ta kai kara su na da yawa su na da bakin da za su zakalkale su juya mata magana, yau da gobe har uba ya fara zargin amarya da tsanar ‘yayansa da matarsa ta fari.

Karshe dai idan amarya ta ji wuya sai ta fita ta bar musu gidan ta bar kananan yaranta su hadu su wahalar da su, sai ta koma gidansu ta yi ta fama da zawarci. Burin uwa da yaranta ya cika an tafi an bar musu gidan su kadai.

Ka da mu manta komai nisan jifa kasa zai fado, haka duk abin da ka cuka shi za ka girba, tabbas bahaushe ya yi gaskiya haka batun ya ke. Idan amarya ta yi hakuri yau da gobe ta na zamanta abin da uwarsu ta koya mu su zai koma kanta domin idan ta na sawa su yiwa amaryarta rashin kunya gobe ita  za su yiwa. Ba ta isa ta hana su ba kuma ba ta da bakin da za ta yi mu su tsawa domin ita da bakinta ta ce su je su zagi babba koma su bangaje matar uba, matar uba kuwa  ai uwa ce a gare su.

Dan haka ka da uwa ta yi mamaki idan yaranta su ka fara yi mata mu su su na yi mata rashin kunya, ta saka su aiki su ki yi, ta dake su su na kokarin ramawa ta zage su su na cewa ba dai nawa ba. Kuma duk yadda za su kai ga lalacewa babu abin da ya shafi uba ke uwa ke ce a ciki tsundum ko da uba ya na jin ciwon abin da su ke yi a ransa ke uwa sai kin fi jin zafi tunda ke ce ki ke yini da kwana tare da su a gida daya kuma a daki daya.

Ba za ki san kin tafka kuskure ba sai sanda ki ka yi musu aure musamman su ka je su ma su ka iske wasu matan a gidan, matan kuma su na da yara, abin da ka cuka fa shi za ka girba, sakayyar Allah kuwa tun daga duniya a ke tsinta, ‘ya’yan miji fa za su takurawa yaranki abin da ba su yi ba ma za’a yi musu, ko wahala da bakin ciki bai sa sun fito ba tabbas za su yi zaman wahala da takaici ba komai ba ne illa hakkin amaryar Mahaifinsu da ya ke bibiyarsu.

Yadda a gidansu su ka gani mahaifiyarsu ba ta mutunta a abokiyar zamanta ta dauke ta abokiyar gabarta duk da biyayyar da amaryar ta ke yi mata a banza, su ma yara sun saka hakan a cikin zuciyarsu dan haka idan su ka tarar da wata a gidan tabbas abokiyar gaba za su dauke ta ayi ta fada, haka kuma idan aka auro mu su  wata daga baya ba za su yarda a zauna lafiya ba, kin ga kenan kin bata tarbiyar zuri’arki gaba daya su ma ‘yayansu haka za su tashi su koyawa ‘ya’yansu haka haka za’ayi ta tafiya har danginku ya sami mummunar shaida a ce kada a auri ire-irenku ma su dukan kishiya ko danbe da kishiya.

Ki sa ni ko ki na raye ko ba kya raye ki na da kwamishon alhaki a dukka rashin tarbiyyar da ya ke faruwa da zalumci da ‘yayanki da jikokinki su ke yi. Ki tuna akwai mutuwa akwai rashin lafiya wannan amarya ita za ta rike yaranki watarana idan ba kya nan, dan haka ki nunawa yaranki ita ma uwarsu ce dole su girmama ta kamar yadda za su girmamaki da mahaifinsu. Idan ki ka yi haka sai kin fi kowa cin ribar abin nan gaba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here