Cacar-bakin da ya barke tsakanin PDP da APC kan abun da ya faru yayin zuwan Buhari Kano

0
30

Jam’iyyar APC mai mulkin Najeriya da babbar jam’iyyar adawa ta PDP na musayar kalamai kan abubuwan da suka faru a lokacin ziyarar shugaba Muhammadu Buhari zuwa jihar Kano.

Hakan na zuwa ne bayan wasu hotuna da aka yaɗa a shafukan sada zumunta, inda ake cewa wasu ne suka yi jefe-jefe a lokacin ziyarar ta shugaban ƙasa domin nuna adawa.

Sai dai jam’iyyar All Progressive Congress ta musanata labaran da ke cewa an kai wa ayarin shugaban na Najeriya hari a lokacin ziyarar ta jihar Kano.

Inda ta ƙara da cewa bayanin da ke cewa an jefi shugaba Buhari wani ƙagaggen labari ne da jam’iyyar Peoples Democratic Party ta ƙirƙira domin zubar da ƙimar shugaban ƙasar.

Tun farko mai magana da yawun kwamitin zaɓen shuigaban ƙasa na jam’iyyar PDP, Sanata Dino Melaye ya wallafa bidiyon da ke iƙirarin cewa an jefi tawagar shugaba Buhari a lokacin ziyarar ta Kano.

Haka nan jam’iyyar PDP, a wata sanarwa da ta fitar, wadda ta samu sa hannun sakataren yaɗa labarunta na ƙasa Hon Debo Ologunagba, ta yi Alla-wadai da abin da ta kira hari kan tawagar shugaban ƙasar.

Inda ta bayyana harin a matsayin wani yunƙuri na yin zagon ƙasa ga fadar shugaban ƙasa, da tayar da husuma, da kuma yin cikas ga babban zaɓen ƙasar na 2023.

Sai dai sanarwar ta ƙara da cewa “babban abin damuwar shi ne yadda ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar APC ke ƙoƙarin illata da kuma kunyata shugaba Buhari a lokacin da yake gudanar da aikinsa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here