Ya kamata mutane su yi amfani da kwanaki 10 wajen mayar da tsofaffin kudin su banki – Sanusi

0
75

Sarkin Kano murabus kuma Khalifan Tijaniyya, Sanusi Lamido Sanusi, ya yi kira ga daukacin ‘yan Nijeriya da ke ajiye da tsofaffin kudade da su yi amfani da karin wa’adin da CBN ya yi don kai tsofaffin kudaden bakunan da suke ajiya.

Ya ce, daga yanzu zuwa ranar 17 ga watan Fabrairu duk mai tsofaffin takardun kudaden ya je ya ajiye su a banki, inda ya yi nuni da cewa, ajiye kudaden a bankunan, zai taimaka wajen yin mu’amala da kudade a Nijeriya.

“CBN ya bayar da tabbacin cewa, zai sa ido a kan bankunan kasar nan don tabbatar an musanya wa kowa tsofaffin kudaden da sabbi.”

Ya bukaci ‘yan Nijeriya da su taimaka wajen sa ido a kan wadanda ke yin cuwa-cuwa a bankuna.

A cewarsa, “Akwai mutanen da ke karbar kudade daga wajen wasu ‘yan siyasa ko masu laifi da ba za su iya zuwa bankuna da sunansu ba don kai tsofaffin kudade.

“Ku kwana da sanin cewa, duk wanda ya dauki kudade masu yawa ya kuma sanya su a cikin asusunsu na ajiya a bankuna, bayan kuma ana sane da cewa, kudaden sun fi karfin a gan su a cikin asusunsa na ajiya, EFCC za ta iya kiransa don yi mata bayanin inda ya samo kudaden.

“Wadanda suka tara kudade ta hanyar zalunci, shi ke nan ta kare masu, wannan alhakkinmu ne ya kama su kuma bai kamata mu tausaya masu ba ko kadan.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here