‘Yan sanda sun bankado maboyar ‘yan bindiga, sun cafke mutum 6 a Nasarawa

0
151

Rundunar ‘yansandan Jihar Nasarawa ta ce ta kai farmaki maboyar masu garkuwa da mutane a kauyen Kiguna da ke cikin garin Lafiya, babban birnin jihar, tare da cafke wasu mutane shida.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Maiyaki Muhammed-Baba, ne ya bayyana hakan a wani taron manema labarai da ya gabatar domin gabatar da nasarorin da rundunar ta samu daga farkon watan Janairu, a ranar Litinin a Lafiya. 

Muhammed-Baba ya ce, a ranar 12 ga watan Janairu da misalin karfe 4:00 na safe, jami’an ‘yan sandan da ke aiki da sashen Assakio, bisa ga bayanan da suka samu, sun kai samame maboyar tare da kama wasu mutane hudu.

“An kwato AK-47 guda daya a cikin gidan, sai kuma sauran makamai da aka kwato,” in ji shi.

Kwamishinan ‘yansandan ya kuma ce a ranar 13 ga watan Janairu, jami’an ‘yansanda daga wannan sashe sun kama shugaban kungiyar masu garkuwa da mutane.

Ya kara da cewa, tun daga farkon shekarar nan zuwa yau, ‘yansanda sun kama wasu mutane 21 da ake zargi da aikata laifuka daban-daban.

Mohammed-Baba ya bayyana wadanda ake zargin sun hada da: ‘yan fashi 16, sai wasu da ake zargin barayin shanu ne guda guda bigu da masu satar babura guda biyu.

Ya lissafa abubuwan baje kolin da aka kwato daga hannun wadanda ake zargin kamar: motoci hudu, makamai da shanu da sauransu.

Kwamishinan, ya ce za a gurfanar da wadanda ake zargin a gaban kotu bayan kammala bincike.

Sai dai ya ce galibin wadanda ake zargin sun amsa laifukan da suka aikata kuma suna taimaka wa ‘yansanda wajen gudanar da bincike.

Mohammed-Baba ya danganta nasarar da rundunar ta samu da goyon bayan jama’a da sarakunan gargajiya da sauran hukumomin tsaro da kuma kafafen yada labarai.

Don haka ya yi kira ga jama’a da su bai wa ‘yansanda sahihin bayanan da za su taimaka musu wajen rage yawaitar aikata laifuka a jihar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here