Hisbah ta amince da sahihancin auren matar da ta auri saurayin ‘yarta a Kano

0
69
Hisbah
Hisbah

Hukamar Hisbah ta jihar Kano ta gamsu da sahihancin Auren da kwamandata mai kula da karamar hukumar Rano ya daura a kwanakin baya da wata bazawara, wacce a shekarun baya, ya ta ba neman yar ta ta da aure kuma hakan bai yu ba.

Da yake mikarahoton binciken kwamatin, shugaban kwatatin kuma mataimakin babban kwamanda hukumar mai kula da aiyuka na musanman, malam Hussain Ahmad Cediyar Kuda shine ya furta hakan a lokacin da yake ga batar da rahotonsa a gaban babban kwamanda a shelkwatan hukumar da ke unguwar sharada.

Yace duba da yadda kwamatin ya gudanar da bincike a tsakanin bangarorin da ake zargi, da aikata tabargaza musanman, wacce aka daura aure, ya kara da cewar dogaro da hujjuji kwara guda biyar Wanda kwamatin ya gano a yayin binciken, shi ya da da tabbatar da sahihancin auren a tsakanin bazawarin da bazawarar.

Hausa24 ta rawaito cewa, lokacin da yake karban kunshin rahoton kwamatin, babban kwamanda hukumar Hisbah na jiha, Dr. Harun Muhammad Sani Ibin Sina ya godewa yan kwamatin bisa nuna gogewa tare da jajircewa domin tantance gaskiyar abinda ake zargi.

Sheik Ibn Sina yayi kira ga jama’a da su guji yada labaran da ba’a tantance sahinhancinsa ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here