Kotu ta aike da Murja Kunya zuwa gidan yari

0
147
Murja Ibrahim Kunya
Murja Ibrahim Kunya

Wata kotu a Kano ta aika da Murja Ibrahim Kunya zuwa gidan gyaran hali.

Murja dai ta shahara musamman a shafin TikTok wurin yin bidiyo.

Tun da farko dai lauyan gwamnati Barrista Lamiɗo Abba Soron Ɗinki ya karanto mata tuhume-tuhumen da ake zarginta da su inda Aisha Najamu da Idris Mai Wushirya suka kai ƙararta inda suka ce ta yi bidiyo wanda ta ci zarafinsu a shafin na TikTok.

Sai dai bayan karanto mata wannan zargin Murja ta musanta wannan zargin, kamar yadda gidan rediyon Freedom ya rawaito.

Haka kuma tuhuma ta biyu ita ce wadda wani lauya Barrista Ali Hamza ya gabatar inda aka zarge ta da yaɗa kalamai na batsa da shiga ta batsa da yunƙurin tayar da hankalin al’ummar jihar Kano.

Lauyan Murja Barrista Zaharadeen ya nemi kotu ta bayar da belinta inda har ya yi roƙo kan a mayar da wannan lamari zuwa hukumar Hisbah amma kotu ba ta amince ba.

A halin yanzu dai an ɗage zaman shari’ar zuwa 16 ga watan Fabrairu domin gabatar da hujjoji da shaidu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here