Kotu ta raba auren ‘yar Ganduje da shafe shekaru 16

0
106

Wata Kotun Shari’ar Musulunci da ke zamanta a Kano a ranar Alhamis ta raba auren Asiya Ganduje, diyar Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, mai shekara 16.

Asiya ta garzaya kotu tana neman a raba aurenta da mijinta, Inuwa Uba, saboda ta gaji ta  da zaman aure wanda suke  da ‘ya’ya hudu.

Alkalin kotun, Khadi Halliru Aliyu ya raba auren ne a lokacin da yake yanke hukunci kan lamarin a ranar Alhamis.

Sai dai Khadi Aliyu ya umarci diyar Ganduje da ta mayar wa mijinta Uba, sadakin N50,000 a matsayin kul’i.

Kotun ta kuma yi watsi da bukatar mijin Asiya na neman takardun kadarorin da ya ce nasa ne.

Lauyan mai kara Ibrahim Nassarawa, ya ce kotun ta yanke hukuncin ne bisa abin da ya ke na shari’ar muslinci  tushen auren wanda shi ne sadaki.

Da yake mayar da martani kan hukuncin, Lauyan maigidan Umar I. Umar ya ce za su yi nazari kan hukuncin kuma za su jira mataki na gaba daga wanda yake karewa kan ko za su kai ga kotun daukaka kara a kan lamarin ko a’a.

Ya ce sun yi iya kokarinsu wajen daidaita ma’auratan amma abin ya ci tura musamman yadda ta haifa masa ‘ya’ya hudu amma abin bai yiwu ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here