Da sabbin kudi muke sayen makamai – ‘Yan bindigar Najeriya

0
127

A Najeriya wani kasurgumin dan ta’adda, Kachalla Balleri, ya ce sun dade wajen amfani da sabbin kudden Naira da aka sauya fasali, hasalima da su suke sayen makamai.

Balleri na daya daga cikin jagororin ‘yan ta’adda da ake nema ruwa a jallo, suna ta’addanci a wasu yankunan jihohin Zamfara, Katsina da Kaduna; da wasu sassan Jamhuriyar Nijar.

An nuna shugaban ‘yan fashin dajin a wani faifan bidiyo yana baje kolin sabbin takardun kudin na naira da aka sake wa fasali.

Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele, ya bayyana cewa manufar sauya fasalin kudin kasar Naira ta kunshi dakile yadda masu garkuwa da mutane ke karban kudin fansa.

To sai cikin faifan bidiyon, Balleri ya ce manufar za ta azabtar da talakawa ne kawai, saboda su ko a jikinsu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here