Sojoji sun fatattaki ‘yan bindiga, sun ceto mutane 30 da aka sace a Kaduna

0
66

Dakarun sojin Nijeriya a Jihar Kaduna sun kama wasu ‘yan bindiga da suka yi garkuwa da matafiya a kauyen Manini da ke kan hanyar Kaduna zuwa Birnin Gwari, inda suka fatattake su.

Sojojin da ke rakiyar babban hafsan horas da ayyuka na tsaro, Manjo Janar SE Udonwa a ziyarar aiki a hedikwatar ‘Operation Whirl Punch’ da ke karamar hukumar Birnin Gwari a Jihar Kaduna, sun yi galaba a kan ‘yan bindigar, lamarin da ya tilastawa ‘yan ta’addan tserewa.

Wata sanarwa da mukaddashin daraktan hulda da jama’a na rundunar soji ta daya, Laftanar Kanar Musa Yahaya ya fitar, ta ce dakarun sojin sun ceto mutane 30 da aka yi garkuwa da su, tare da kwato babura guda biyu, kuma nan take suka bude babbar hanyar domin zirga-zirgar ababen hawa.

Sanarwar ta ce, an raka wadanda aka ceto zuwa Udawa da Birnin Gwari.

A halin da ake ciki, Kanar Yahaya ya kara da cewa babban jami’in horas da ayyukan tsaro na rundunar, Manjo Janar Udonwa, ya yaba wa sojojin bisa kwarewar da suka nuna da kuma jajircewarsu wajen gudanar da aikin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here